- Hani daga shiga gun ajanibai da kaɗaitaka da su, dan toshe kafar afkawa cikin alfasha.
- Wannan mai gamewa ne a duk wani da ba mararrami ba na ɗan uwan miji da makusantansa, waɗanda su ba muharraman matar ba ne, kuma babu makawa da izina ta shigar ta zama mai kaiwa ce zuwa ga kaɗaitakarsu.
- Nisanta daga wuraren zamiya mai gamewane, dan tsoron afkawa cikin sharri.
- Al-Nawawi ya ce: Ma'abota ilimi na luga sun haɗu akan cewa al-Ahma'u (su ne) 'yan uwan mijin mace kamar babansa da baffansa, da ɗan uwansa da ɗan ɗan uwansa, da ɗan baffansa da makamancinsu, kuma al-Aktan (su ne) 'yan uwan matar mutum, surukai kuma sun haɗa nau'i biyun.
- Ya kamanta (ɗan uwan miji) da mutuwa, Ibnu Hajar ya ce; Larabawa suna siffanta abinda ake ƙi da mutuwa, ta fuskar kamanceceniyar cewa ita mutuwa ce a Addini idan saɓo ya afku, kuma mutuwar wacce aka keɓanta da ita ce idan saɓo ya afku kuma jifa ya wajaba, kuma halakar mace da rabuwar mijinta idan kishi ya ɗaike shi akan sakinta.