- Rashin cancantar mutum yana zama kodai saboda baccin da rashin farkawa ya sarayar masa da wajibansa, ko saboda ƙarancin shekaru da yarinta wanda hakan ya sa ya rasa cancanta, ko saboda haukan da ayyukansa na hankali suka raurawa tare da shi, ko abinda yake riskarsa kamar maye, wanda ya rasa banbancewa da fayyacewa ingantacciya, to cancanta ta koru daga gare shi saboda sababi daga waɗannan sabubban uku; domin Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - saboda adalcinSa, da haƙurinSa, da kyautarSa, haƙiƙa Ya ɗauke masa kamun abinda yake bijirowa daga gare shi na wuce gona da iri ko gajiyawa a cikin hakkin Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Rashin rubuta zunubai akansu, ba ya kore tabbatar da hukunce-hukunce na duniya akansu; kamar mahaukaci da zai yi kisa, to babu sakayya akansa kuma babu kaffara, amma akwai diyya akan 'yan uwansa.
- Balaga tana da almomi biyar: Fitar maniyyi, ta hanyar mafarki da waninsa, ko tsirowar gashin mara, ko cika shekara goma sha biyar, mace ta ƙara al'amari na huɗu: Shi ne haila.
- Al-Subki ya ce: Ƙaramin yaro shi ne yaro.
- Waninsa ya ce; Yaro a cikin mahaifyarsa ana ambatansa ɗan tayi, idan aka haife shi to ya zama yaro, idan an yaye shi to ya zama yaro har zuwa shekara bakwai, sannan ya zama mai tasowa har zuwa shekara goma sannan ƙaƙƙarfan yaro, wanda ake yankewa da shi cewa ana ambatansa yaro a cikin waɗannan halayen gaba ɗayansu, Suyuɗine ya faɗe shi.