- Haramcin sanya alhariri da dibaji ga maza, da kuma narko mai tsanani akan wanda ya sanya shi.
- An halastawa mata alhariri da dibaji.
- Haramcin ci da sha a farantan zinari da azirfa da kuma kofunan su akan maza da mata.
- Kausasawar Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - a inkari, kuma ya bayyana hakan da cewa shi ya hana shi ne sama da sau ɗaya daga amfani da zinari da azirfa, sai dai shi din bai hanu ba.