- Waliyyi sharaɗi ne a ingancin aure, idan aure ya faru ba tare da waliyyi ba, ko mace ta aurar da kanta, to, aurenta bai inagnta ba.
- Waliyyi shi ne mafi kusancin mazaje ga mace, wani waliyyi na nesa ba zai aurar da ita ba, tare da samuwar waliyyi na kusa.
- An sharɗanta (wasu) sharuɗɗa ga waliyyi: Ya zama mukallafi, kuma namiji, da shiriya a sanin maslahohin aure, da haɗuwar Addini tsakanin waliyyi da wanda zai yi wa walicci, duk wanda bai siffantu da waɗannan siffofin ba, to bai cancanci zama waliyyi a ɗaura aure ba.