- Wajibcin cika sharuɗɗa wanda ɗayan ma’aurata ya sa, sai dai sharaɗin da ya haramta halal, ko ya halatta haram.
- Cika sharuɗɗan aure ya fi sauran ƙarfi, domin yana matsayin halatta farji ne.
- Girman matsayin aure a Musulunci ta yadda ya fi kowanne sharaɗi ƙarfin cikawa.