- Halaccin jin daɗi da abubuwa na halak a duniya wanda Allah Ya halatta wa bayinSa ba tare da ɓarna ko gadara ba.
- Kwaɗaitarwa a kan zaɓin mace ta kwarai, domin taimako ce ga mijinta wajen biyayya ga Ubangijinsa.
- Mafificin jin daɗin duniya shi ne abin da ya kasance a kan bin Allah, ko ya taimaka a kan hakan.