Daga Abu Burzata Al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Diga-digan bawa ba z...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani mutum daga mutane da zai ketare matsayar hisabi a ranar Alkiyam...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mai kai kawo ga wacce mijinta...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake tsayuwa akan al’amuran matar da mijinta ya rasu alhali ba ta...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce : "Wanda ya kasance ya yi imani da...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa bawan da ya yi imani da Allah da ranar lahira wadda makomarsa take a cikinta,...
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi -ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce da ni: "Kada ka wulaƙanta komai daga wani a...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya kwaɗaitar a kan aikin alheri, kuma kada ya wulaƙantashi ko da ya kasance kaɗan ne, daga wann...
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na hore ku da gaskiya,...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da gaskiya, kuma ya bada labarin cewa lazimtarta yana kaiwa zuwa aiki na gari mada...
Daga Abu Burzata Al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce : "Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya faɗi alheri ko ya yi shiru, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama maƙocinsa, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama baƙonsa".
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi -ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce da ni: "Kada ka wulaƙanta komai daga wani aikin alheri, ko da ka gamu da ɗan uwanka ne da sakakkiyar fuska".
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na hore ku da gaskiya, saboda gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna, kuma mutum ba zai gushe ba yana yin gaskiya, kuma yana kirdadon gaskiya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan gaskiya ne.
Kuma na haneku da ƙarya, saboda ƙarya tana shiryarwa ne zuwa ga fajirci, kuma fajirci yana shiryarwa ne zuwa ga wuta, mutum ba zai gushe ba yana yin ƙarya kuma yana kirdadon ƙarya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan ƙarya".
Daga Jariri ɗan Abbdullah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba".
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku".
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi ".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Hakkin musulmi akan musulmi guda biyar ne: Maida sallama, da gaida mara lafiya, da bin jana'iza, da amsa gayyata, da gaida mai atishawa".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba za ku shiga aljanna ba har sai kun yi imani, Ba za ku yi imani ba har sai kun so junanku, , shin ba na shiryar daku akan abinda idan kun aikata shi za ku so junanku ba? ku yada sallama a tsakaninku".
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su -: Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba".
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakurai da shi ba, kuma Yake ɗaukaka darajoji da shi?" Suka ce: Na'am, ya Manzon Allah, ya ce: "Cika alwala a lokutan da ake ƙi, da yawan takawa zuwa masallatai, da jiran sallah bayan sallah, wadannan su ne shi ne zaman dako".