- Gaskiya ɗabi'a ce mai girma tana samuwa ne ta hanyar aiki da ƙoƙari, domin cewa mutum ba zai gusheba yana gaskiya kuma yana kardadon gaskiya, har sai gaskiya ta zama ɗabi'a gare shi, sai a rubuta shi a wurin Allah cikin masu yawan gaskiya kuma mutanen kirki.
- Ƙarya ɗabi'a ce abar zargi mai ita yana samuntane saboda tsawon gogayyarsa, da kardadonsa a faɗa da aikatawa, har sai ta wayi gari ɗabi'a, sannan a rubuta shi cikin maƙaryata a gurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Gaskiya ana fadinta ne akan gaskiyar harshe, ita ce kishiyar ƙarya, da gaskiya a niyya ita ce ikhlasi, da gaskiya a ƙudirin niyya akan alheri da ya yi niyyarsa, da gaskiya a cikin ayyuka, mafi ƙarancinta daidaituwar zahirinsa da badininsa.
- Da gaskiya a matakai, kamar gaskiya a tsoro da ƙauna da wasunsu, wanda ya siffantu da hakan to ya zama mai yawan gaskiya, ko (ya siffantu) da wasu daga cikinsu to ya zama mai gaskiya.