- Kwadaitarwa akan taimamkekeniya da toshe bukatun masu rauni.
- Ibada ta kunshi kowane aiki na gari, daga ibada akwai kaikawo ga wacce mijinta ya rasu da kuma miskini.
- Dan Hubaira ya ce: Abin nufi cewa Allah - Madaukakin sarki - Zai tattaro masa ladan mai azimi da mai tsayuwar (dare) alokaci daya; saboda shi ya tsaya ga matar da mijinta ya rasu a matsayin mijinta..., ya kuma tsaya ga miskinin da ya gajiya daga tsayuwa akan kansa, sai ya ciyar da wannan ragowar abincinsa, ya kuma yi sadaka da karfinsa, sai amfaninsa ya zama ya yi daidai da azimi da tsayuwar dare da kuma yaki.