- Addinin Musulunci addini ne na rahama, shi gabaɗayansa a tsaye yake a kan biyayya ga Allah da kyautatawa zuwa ga halitta.
- Allah -Mai girma da ɗaukaka - Mai siffantuwa ne da rahama, kuma tsarki ya tabbatar maSa Shi ne Mai rahama a duniya Mai rahama a lahira, Mai sadar da rahama ne ga bayinSa.
- Sakayya tana daga jinsin aiki, masu jin ƙai Allah Yana jin ƙansu.