- Jin ƙai abin nema ne ga sauran ababen halitta, sai dai an keɓanci mutane da ambato ne don ba da muhimmanci garesu.
- Allah Shi ne Mai jin ƙai, kuma Yana jin ƙan bayinsa masu jin ƙai, to, sakamako yana kasancewa ne daga jinsin aiki.
- Jin ƙai ga mutane ya tattaro alheri garesu da tunkuɗe sharri garesu da mu'amalantarsu da kykkyawa.