- Imani da Allah da ranar lahira asali ne ga kowane alheri, kuma yana zaburarwa a kan aikin alheri.
- Gargaɗi daga illolin harshe.
- Addinin musulunci addinin sabo ne da karamci
- Waɗannan ɗabi'un suna daga yankin imani kuma daga ladubba ababen yabo.
- Yawaita zance zai iya kai wa zuwa abin ƙi ko abin haramtawa, kuɓuta tana cikin rashin magana sai ta alheri.