- Falalar soyayya a tsakanin muminai da murmushi da walwala a yayin haɗuwa.
- Cikar wannan shari'ar da tattarowarta, kuma ita ta zo da dukkanin abin da a cikinsa akwai gyara musulmai da haɗe kansu.
- Kwaɗaitarwa a kan aikata aikin alheri ko da ya ƙaranta.
- An so shigar da farin ciki ga musulmai; saboda abin da ke cikin hakan na tabbatar da sabo a tsakaninsu.