- Shiga aljanna ba ya kasancewa saida imani.
- Daga cikar imani musulmi ya so wa dan uwansa abinda yake sowa kansa.
- An so yada sallama da shinfidata ga musulmai; dan abinda ke cikinta na yada soyayya da aminci tsakanin mutane.
- Ba'ayin sallama sai ga musulmi; saboda fadinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi -: "A tsakaninku".
- Yada sallam Akwai dauke damuwa da kauracewa da gaba ta hanyar yin sallama.
- Muhimmancin soyayya tsakanin musulmai, kuma cewa ita tana daga cikar imani.
- Ya zo a cikin wani hadisin daban cewa sigar sallama cikakkiya: "Assalamu alaiku warahmatullahi wa barakatuh ", ya isa a ce: "Assalamu alaikum".