Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake k...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi kusancin lokacin da bawa yake kusanci ga Ubangijinsa shi ne alhalin yana...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita addu'a da addu'a gamammiya, daga cikinsu: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu...
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na baku labari da mafificin...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: .
Shin kuna son in baku labari ? In sanar da ku da mafificin ayyukan...
Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na w...
Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata...
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wa shinfida...
Ya kasance daga shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan ya zo wa shinfidarsa dan ya yi bacci yana tara tafikansa biyu sai ya d...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa ga Ubangijinsa shi ne idan yana mai sujjada, sai ku yawaita addu'a".
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta".
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku kuma mafi alheri agareku daga ciyar da zinari da azirfa, kuma mafi alheri agareku daga ku haɗu da maƙiyanku ku daki wuyan su, suma su daki wuyan ku?" suka ce: Eh. Ya ce: "Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki".
Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, sai ya ce: "Haƙiƙa ka tambayeni daga wani abu mai girma, kuma shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa, ka bautawa Allah kada ka yi shirka da komai da Shi, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin Allah”, sannan ya ce: "Shin ba na shiryar dakai ba ga ƙofofin alheri: Azimi garkuwa ne, sadaka tana kashe kuskure kamar yanda ruwa yake kashe wuta, da sallar mutum a tsakiyar dare" ya ce: Sannan ya karanta: "{Sasanninsu suna nisanta daga makwantansu}, har yakai {Suke aikatawa}".
Sannan ya ce: "Shin bana baka labari da asalin al'amari gaba dayansa ba da ginshikinsa, da kololuwar tozansa?" Na ce: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: "Asalin al'amari Musulunci, kuma ginshikinsa sallah, kuma kololuwar tozansa Jihadi" sannan ya ce: "Shin bana baka labari da abinda zai tattaro hakan gaba dayansa ba?" na ce: Eh, Ya Manzon Allah, sai ya rike harshensa ya ce: "Ka rike wannan", na ce Shin za’a kama mu da abinda muke magana da shi? ya ce: "Babarka ta yi wabinka ya Mu'az, ai ba wani abu ne yake afka mutane cikin wuta ta fuskokinsu ko ta hancinansu ba sai abinda harasansu suke girba".
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wa shinfidarsa kowanne dare yana taro tafikansa, sannan ya yi tofi a cikin su, sai ya karanta a cikinsu: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadi }, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane} (Kul huwa da Falaki da kuma Nasi), Sannan ya shafi abinda ya yi wu daga jikinsa, yana farawa ne da su daga kansa da fuskarsa da abinda ya yi gaba na jikinsa, yanayin haka sau uku.
Daga Shaddadu Dan Aws - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Shugaban Istighfari shi ne ka ce: Ya Allah Kai ne Ubanjina babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai ka halicceni, kuma ni bawanKa ne, kuma ni ina kan alkawarinKa gwargwadon ikona, ina neman tsarinKa daga sharrin abinda na aikata, ina ikirari gareKa da ni'amarKa gareni, kuma ina ikirari da zunubina, to Ka gafarta mini domin cewa babu mai gafartawa sai Kai".
ya ce: "wanda ya fadeta da rana yana mai sakankancewa da ita, sai ya mutu a wannan rana kafin ya yi yammaci to yana cikin 'yan aljanna, wanda ya fadeta da daddare yana mai sakankancewa da ita sai ya mutu kafin ya wayi gari to yana cikin 'yan aljanna".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Cewa shi ya kasance idan ya wayi gari yana cewa: "Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa" Idan ya shiga maraice ya ce: "Da (kiyayewarka) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (al'amarin) Ka zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gare Ka" ya ce: Wani lokaci kuma: "Makoma tana gare Ka".
Daga Aban ɗan Usman ya ce: Na ji Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - yana cewa: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wanda ya ce: Da suna Allah wanda wani abu ba ya cutuwa tare da sunanSa a cikin ƙasa, ko cikin sama, Shi ne Mai yawan ji Masani”. sau uku, wani bala'i na fuj'a ba zai same shi ba har sai ya wayi gari, wanda ya faɗeta lokacin da ya wayi gari sau uku, wani bala'i na fuj'a ba zai same shi ba har sai shiga maraice", ya ce: Sai shanyewar ɓarin jiki ya samu Aban ɗan Usman, sai mutumin da ya ji hadisin daga gare shi ya fara kallonsa, sai ya ce masa: Me yasa meka kake kallona? Na rantse da Allah ban yi wa Usman ƙarya ba, kuma Usman bai yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya ba, sai dai ranar da abinda ya sameni ya sameni a cikinta na yi fushi sai na manta ban fadi addu'ar.
Daga Abdullah dan Khubaib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce: Mun fita cikin dare da akai ruwa da duhu mai tsanani, muna neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallah, ya ce: Sai na riske shi, sai ya ce: "Ka ce", ban cekomai ba, sannan ya ce: "Ka ce", ban ce komai ba, sai ya ce: "Ka ce" sai na ce: Me zan ce? Ya ce: Ka ce: "{Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da falaki da Nasi (Wato ka karanta Qul huwa da Falaki da Nasi) lokacin da ka wayi gari da kuma lokacin da ka yi maraice sau uku sun isheka komai".
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na rasa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wani dare a shinfiɗa sai na lalube shi sai hannuna ya faɗa akan cikin diga-digansa alhali shi yana cikin masallaci alhali su suna a kafe, alhali shi yana cewa: "Ya Allah ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da kuma rangwaminKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gareKa ba zan iya ƙididdige yabo gareKa ba kamar yadda Ka yabi kanKa".
Daga Samura ɗan Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gagreshi - ya ce: "Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma, da kowanne ka fara daga cikinsu ba ya cutar da kai".
Daga Abu Ayyub Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, mulki na sa ne, godiya ta sa ce, Shi mai iko ne a kan komai. Sau goma . zai kasance kamar wanda ya ‘yanta mutane huɗu daga tsatsan (Annabi) Isma’il.