- An so waɗannan addu'o'in a cikin sujjada.
- Mirak ya ce: A cikin ɗaya daga riwayoyi al-Nasa'i: Ya kasance yana faɗin wannan addu'ar idan ya gama sallarsa ya koma makwancinsa.
- An so yabo ga Allah da siffofinSa da kuma roƙonSa da sunayenSa tabbatattu a cikin Littafi da Sunnah.
- A cikinsa akwai girmama Mahalicci a cikin ruku'u da sujjada.
- Halaccin neman tsari da siffofin Allah, kamar yadda neman tsari da zatinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - yake halatta.
- AlKhaɗɗabi ya ce: A cikin wannan maganar akwai ma’ana mai kyau, ita ce: Cewa shi haƙiƙa ya nemi tsarin Allah Ya tsare shi da yardarSa daga fushinSa, da kuma rangwaminSa daga uƙubarSa, yarda da fushi kishiyoyi ne masu fuskantar juna, haka nan rangwami da kamu da uƙuba, lokacin da ya zama zuwa anbatan abinda bask shi da kishiya Shi ne Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ya nemi tsari da Shi daga gareShi bada waninSa ba, ma'anar haka: Istigfari domin kasawa wurin cika wajibi daga haƙƙin bayinSa, da yabo a gareShi. da faɗinSa: ba zan iya ƙididdige yabo a gareka ba: Wato ba zan iya shi ba, kuma ba zan iya kai matuka a cikinsa ba.