- An so wannan addu'ar safe da yamma, dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Buƙatuwar bawa ga Ubangijinsa a cikin dukkan halayensa da lokutansa.
- Abin da yafi a karanta zikirai, a safiya: Daga ɓollowar alfijir zuwa ɓullowar rana a farkon yini, haka kuma daga bayan la'asar zuwa kafin faɗuwar rana, idan ya faɗesu bayan hakan yana nufin: -Ya faɗesu a safiya bayan ɗagawar walaha - ya isar masa, idan ya faɗesu bayan azahar ya isar masa, idan ya faɗesu bayan Magariba ya isar masa, to wannan lokaci ne na zikiri.
- Munasabar faɗinsa: " Tashi yana gare Ka" da safe, wannan yana tunatar da shi da rayuwa da tashi babba lokacin da mutane zasu mutu kuma a tashesu ranar alƙiyama, to wannan tashine sabo, kuma yini ne sabo da ake dawo da rayuka a cikinsa, kuma mutane suke watsuwa a cikinsa, wannan sabuwar safiyar wacce Allah Ya halicceta zata nunfasa; dan ta zama mai shaida akan ɗan Adam, kuma lokutansa da sakwankwaninsa su zama taskar ayyukansa.
- Munasabar faɗinsa: "Makoma tana gareKa" da yamma, lokacin da mutane suke dawowa daga ayyukansu da watsuwarsu a abubuwan maslahohinsu da rayuwarsu, zasu dawo zuwa gidajensu, zasu dawo zuwa hutu bayan sun rarrabu, sai ya tuna makoma da komawa zuwa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -