- Muhimmancin kiyayewa akan sallar jam’i a cikin masallaci, da himmantuwa da salloli, da rashin shagaltuwa daga barin su.
- Kyakkyawan tsarin karantarwar annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - da kwaɗaitarwarsa ga sahabbansa ta inda ya fara su da lada mai girma ta hanyar tambaya, wannan wata hanya ce daga hanyoyin koyarwa.
- Fa'idar bijiro da tambaya da amsa: Zance yana kama zuciya a tsarin hukuncin a boye kafin a bayyana.
- (Imam) Nawawi - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Wadancan su ne zaman dako, wato: Zaman dako wanda aka kwaɗaitar a cikinsa, kuma asalin zaman dako tsare abu, kamar shi ya tsare ransa akan wannan ɗa'ar, an ce: Lallai cewa shi ne mafificin zaman dako kamar yadda aka ce: Jihadi jihadin rai, zai iya yiwuwa cewa shi ne zaman dako wanda ya sawwaƙa wanda zai yi wu, wato: Lallai cewa shi yana daga nau'o'in zaman dako.
- An maimaita kalmar "Zaman dako" kuma an yi mata Ma'arifa da (Al) ta ta'arifi; hakan girmamawa ce ga sha'anin waɗannan ayyukan.