- Kwaɗaitarwa akan rintse ido.
- Gargaɗi akan dawwamar da gani akan abinda yake haramta gare shi, idan ganinsa ya afku bagatatan kuma ba tare da nufi ba.
- A cikinsa kuma akwai haramcin duba zuwa ga mace wani al’amari ne tabbatacce a gurin sahabbai saboda dalilin cewa Jarir - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga abinda da ganinsa ya afka akan wata mace ba tare da nufi ba, shin hukuncinsa hukuncin wanda ya yi nufin gani ne?
- A cikinsa akwai kulawar shari'a ga maslahohin bayi, cewa ita ta haramta musu kallo zuwa ga mata saboda abinda yake biyo baya akansa na ɓarna iri daban daban na duniya da lahira.
- Komawar sahabbai zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da tambayarsa game da abinda yake rikitar da su, haka nan yana kamata ga kowa da kowa komawa zuwa ga malumansu da tambayarsu game da abinda ya rikitar da su.