- Halaccin layya, haƙiƙa musulmai sun haɗu akanta.
- Abin da ya fi layya ta zama daga wannan nau'in da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da shi; dan kyan ganinsa da kuma kasancewar kitsensa da namansa yafi daɗi.
- AlNawawi ya ce: A cikinsa cewa an so mutum ya jiɓinci yanka layyarsa da kansa, kada ya wakilta a yankata sai da wani uzuri, a wannan lokacin an so ya halacci yankanta, idan ya wakilta wani musulmi ya halatta babu wani saɓani.
- Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai son kabbara tare da basmala a lokacin yanka da son ɗora ƙafar dama akan fatar wuyan abin layyar, kuma sun haɗu akan cewa kwantar da ita yana kasancewa ne a ɓangaren hagu sai ya ɗora ƙafaresa akan ɓangaren dama dan ya zama ya fi sauƙi ga mai yankan a wurin riƙe wuƙa da dama, da riƙe kanta da hannunsa na hagu.
- An so layya da mai ƙaho kuma yana halatta da waninsa.