- Falalar ayyuka na ƙwarai a goman farko Zul Hijja, ya wajaba a kan Musulmi ya ribaci waɗannan kwanakin, ya yawaita ayyuka na biyayya, kamar anbaton Allah maɗaukaki, da karatun Alkur’ani, da hailala da hamdala, da kuma Sallah da sadaka da Azumi da sauran ayyukan alheri.