- Kulawa da gyara zuciya, da tsarkaketa daga dukkanin wata siffa abar zargi.
- Gyaran zuciya ta hanyar ikhlasi ne, gyaran aiki kuma ta hanyar bin Annabi ne - tsira da aminci su tabbata a gare shi -, su ne abin dubawa da lura a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Kada mutum ya ruɗu da dukiyarsa ko kyawunsa ko jikinsa ko wani abu daga abubuwan wannan duniyar.
- Gargaɗi daga karkata zuwa zahiri ba tare da gyara baɗini ba.