- Shar’antuwar Talbiyyah a Hajji da Umarah, da ƙarfafuwarta a cikinsa; domin ita Talbiya alamarsa ce keɓantacciya, kamar kabbara alama ce ta sallah.
- Ibnul Munir ya ce: A cikin Shar’antuwar Talbiyyah akwai faɗakarwa akan girmamawa ga Allah - Maɗaukakin sarki - ga bayinSa cewa taruwarsu a ɗakinSa kaɗai ya kasance ne da kira daga gareShi - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
- Abinda ya fi shi ne lazimtar Talbiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma babu laifi da ƙari dan tabbatarwar Annabi - tsira da aminci su tabbata gare shi - ga karin.
- Ibnu Hajar ya ce: Wannan shi ne mafi daidaituwar fuskoki, sai a ware abinda ya zo Marfu'i, idan ya zaɓi faɗar abinda ya zo Mauƙufi ko shi ya farar da shi da kansa daga abinda ya dace to ya faɗe shi a ware dan kada ya cakuɗa da Marfu'i, sai ya yi kama da halin addu'a a tahiya, cewa shi ya ce a cikinsa; Sannan ya zaɓi abinda ya so na roƙo da yabo: wato bayan ya gama da Marfu'in.
- An so ɗaga murya a Talbiyya, wannan a haƙƙin namiji ne kadai, amma mace sai ta ƙanƙar da muryarta dan tsoron fitina.