- Ma'abota ilimi sun haɗu akan cewa daga abinda yake riskar mutum bayan mutuwarsa na lada: Sadaka mai gudana, da ilimin da ake anfanuwa da shi, da addu'a, kuma ya zo a cikin wasu Hadisan daban: Hajji kuma.
- An keɓanci waɗannan ukun da ambato a cikin wannan Hadisin; domin sune tushen alheri, kuma mafi rinjayar abinda ma'abota falala suke nufin wanzuwarsa bayansu.
- Dukkan ilimin da ake anfanuwa da shi to shi lada yana samuwa gare shi, sai dai ƙololuwarsu shi ne ilimi na shari'a da ilimummuka masu ƙarfafarsa.
- Ilimi mafi anfani shi ne waɗannan ukun; domin ilimi mutumin da yake neman saninsa yana anfanuwa da shi, akwai kiyaye shari'a a cikin ilimi, akwai anfanar halitta a gamewa, shi ne mafi ƙunsa kuma mafi gamewa; domin shi yana neman iliminka samamme a cikin rayuwarka kuma samamme bayan mutuwarka.
- Kwaɗaitarwa akan tarbiyyar yara salihai; su ne waɗanda suke anfanar iyayensu a lahira, daga anfanar su suna yi musu addu'a.
- Kwaɗaitarwa akan kyautatawa mahaifa bayan mutuwarsu, shima yana daga aikin alherin ɗa zai anfana da shi.
- Addu'a tana anfanar mamaci koda daga wanin ɗa ne, sai dai ankeɓanci ɗa da ambato; domin shi ne wanda yake ci gaba a addu'a ga mutum a galibi har zuwa mutuwarsa.