- Falalar azimi kuma shi yana kiyaye maishi a duniya daga sha'awowi, a lahira kuma daga azabar wuta.
- Daga ladubban azimi barin zancen alfasha da zancen mara anfani, da kuma haƙuri akan cutarwar mutane da fuskantar munanawarsu da yin haƙuri da kuma kyautatawa.
- Mai azimi ko mai ibada idan ya yi farin ciki saboda cikar bautarsa da kuma ƙarewa daga gareta to hakan ba zai tauye ladansa a lahira ba.
- Cikakken farin ciki shi ne na haɗuwa da Allah - Maɗaukakin sarki -, lokacin da ake cika wa masu haƙuri da masu azimi ladansu ba tare da hisabi ba.
- Sanar da mutane aikin ɗa'a a lokacin buƙata da maslaha ba ya daga cikin riya saboda faɗinsa: (Lallai ni mai azimi ne).
- Mai azimin da ya cika aziminsa shi ne wanda gaɓɓansa suka yi azimi daga zunubai, kuma harshensa daga ƙarya da alfasha, da faɗin zur, cikinsa kuma daga abin ci da abin sha.
- Karfafawar hani daga zance mara anfani da husuma da ihu a lokacin azimi, inba haka ba to wanda ba ya azimi ma an hana shi hakan.
- Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu abubuwan da Alƙur’ani ya keɓannta da su a cikinsa, waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karanta shi, da yin tsarki sabo da shi da I’IJAZ (ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.