- Nau’ukan da aka ambata a cikin wannan hadisin guda biyar ne: Zinare da azirfa da alkama da wake da sha'ir da dabino, idan ciniki ya tabbata a su sinfin to babu makawa dan inagancin cinikin daga sharuɗɗa biyu: Karɓa a majalasin ƙulla cinikin, da kuma daidaito a awo, kamar zinare da zinare, inba haka bafa zai zama riba ta fifiko, idan sun saɓa kamar azirfa da alkama misali to sharaɗi ɗaya ne dan ingancin ƙulla cinikin, shi ne karɓar kuɗin a majalasin ƙulla cinikin, inba haka bafa zai zama riba ta jinkiri.
- Ana nufi da majalasin ƙulla ciniki: Gurin ciniki, daidai ne sun kasance a zaune, ko suna tafiya, ko akan abin hawa, kuma ana nufi da rabuwa abinda ake ɗauka a matsayin rabuwa a al'ada tsakaknin mutane.
- Hani a cikin hadisin ya ƙunshi dukkan nau'ikan zinaren da aka kera da wasunsu, da kuma dukkan azirfar da aka kera da wacce ba'a kera ba.
- Takardun kudade a wannan zamanin yana tabbata a cikinsu abinda yake tabbata acikin saida zinare da a zirfa, wato idan ka yi nufin canja wani kuɗi da wani kuɗin daban kamar riyal da dirhami to fifiko ya halatta da abinda masu ƙulla cinikin suka yarda da shi, sai dai karɓa yana wajaba a wurin siyarwar, inba haka ba to cinikin ya ɓaci, mu'amalar ta zama riba wacce haramta.
- Mu'amaloli na riba basa halatta, kuma ƙullasu ɓatacce ne koda masu cinikin sun yarda; domin Musulunci yana kiyaye haƙƙin mutum da haƙƙin zamantakewa koda shi ya haƙura na shi.
- Hani daga abin ƙi da kuma hana shi ga wanda zai iya hakan.
- Anbatan dalili a lokacin inkarin abin ƙi, kamar yadda Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya yi.