- Zakkar fidda kai ta azimi tana wajaba a fitar wa yaro ita da babba, da ɗa da bawa, kuma ana yi wa waliyyin (yaro) da mamallakin (bawa) umarni da ita, kuma mutum yana fitarwa kansa da 'ya'yansa da wanda ciyarwarsu take wajaba akansa.
- Zakkar fidda kai ba ta wajaba daga ɗan tayi, saidai an so (a fitar masa).
- Bayanin abinda ake fitarwa a zakkar fidda kai, shi ne abincin mutane na al'ada.
- Wajabcin fidda ita kafin sallar idi, abinda ya fi ta kasance a safiyar idi, kuma fitar da ita yana halatta kafin idi da kwana ɗaya ko kwanaki biyu.