Wanda ya saurarawa wanda yake cikin mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (da bashinsa), Allah Zai inuwantar da shi a ranar Alƙiyama ƙarƙashin inuwarssa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya saurarawa wanda yake cikin mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (da bashinsa), Allah Zai inuwantar da shi a ranar Alƙiyama ƙarƙashin inuwarssa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa".
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah - su tabbata agare shi - ya ba da labari cewa wanda ya saurarawa wanda ake bi bashi, ko ya sarayar masa daga bashinsa, to, sakamakonsa: shi ne Allah Zai inuwantar da shi ƙarƙashin al-Arshinsa a ranar Alƙiyama, wanda rana zata kusanto kawunan bayi a cikinta, kuma zafinta zai tsananta akansu. Babu wanda zai samu wata inuwa sai wanda Allah Ya inuwantar da shi.
Hadeeth benefits
Falalar saukakawa bayin Allah - Maɗaukakin sarki -, kuma hakan yana daga sabubban da suke tseratarwa daga tsorace-tsoracen ranar alƙiyama.
Sakamako yana kasancewa daga jinsin aiki.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others