- Wanan neman tsarin yana daga muhimman addu'o'i kuma gamammu, dan abinda suka kunsa na neman tsari daga sharrukan duniya da lahira.
- Tabbatar da azabar kabari kuma cewa ita gaskiya ce.
- Hadarin fitintinu da muhimmancin neman taimakon Allah da addu'a dan tsira daga garesu.
- Tabbatar da fitowar Dujal da girman fitinarsa.
- An so yin wannan addu'ar bayan tahiyar karshe.
- An so yin addu'a bayan aiki na gari.