Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangijina Ka gafarta mini, ya Ubangijina Ka gafarta min'
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangijina Ka gafarta mini, ya Ubangijina Ka gafarta min'.
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a yayin zama a tsakaknin sujjada biyu: Ya Ubangina ka gafarta min, yana maimaita ta.
Ma'anar ya Ubangijina Ka gafarta min: Bawa yana neman daga Ubangijinsa ya shafe masa zunubansa ya suturta aibukansa.
Hadeeth benefits
Shar’antuwar wannan addu'ar a tsakanin sujjada biyu a sallar farilla da nafila.
An so maimaita faɗin: Ya Ubangijina Ka gafarta min, wajibi (shi ne) sau ɗaya.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others