Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Lallai alƙawarin da ke tsakanin m...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa alƙawari tsakanin musulmai da wasunsu daga kafirai da munafikai (shi ne) sa...
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai tsakanin mutum da shirka...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargaɗi game da barin sallar farilla, ya ba da labarin cewa tsakanin mutum da afkawa a s...
Daga Salim ɗan Abulja'ad ya ce: Wani mutum ya ce: Ina ma dai na yi sallah in huta, kamar cewa su (sauran mutanen) sun aibata masa hakan, sai ya ce: Na...
Wani mutum daga sahabbai ya ce: Ina ma na yi sallah in huta, kai ka ce waɗanda ke gefensa sun aibata hakan gare shi , sai ya ce: Na ji Manzon Allah -...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya yi kabbara a sallah, sai y...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi kabbarar sallah yana yin shiru kaɗan kafin ya karanta fatiha, yana buɗe s...
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kaf...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana ɗaga hannayensa agurare uku a sallah, daura da kafaɗa wanda shi ne: Matattarar...
Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta".
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah".
Daga Salim ɗan Abulja'ad ya ce: Wani mutum ya ce: Ina ma dai na yi sallah in huta, kamar cewa su (sauran mutanen) sun aibata masa hakan, sai ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ya Bilai, ka yi iƙamar sallah, ka hutar da mu da ita".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya yi kabbara a sallah, sai ya yi shiru ɗan wani lokaci gabanin fara karatu, sai na ce: Ya manzon Allah, fansarka baba na da Baba ta, kana ganin shirun da kake yi tsakanin kabbara da karatu, me kake cewa? ya ce: Ina cewa: Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwan ƙanƙara kuma mai tsananin sanyi".
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah, haka nan in zai yi kabbara dan ruku'u, haka idan kuma zai ɗago kansa daga ruku'u sai ya ɗagasu, kuma ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gare ka, ya kasance ba ya yin haka a cikin sujjada.
Daga Ubadah dan Samit - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu sallah ga wanda bai karanta Fatiha ba".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo, sai ya yi sallah, sannan (ya zo) ya yi sallama ga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi-sai ya amsa masa kuma ya ce: Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba", sai ya koma ya yi sallah kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo ya yi sallama ga-Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Koma ka yi sallah, domin cewa kai baka yi sallah ba" sau uku, sai ya ce: Na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan iya yin wacce ta fita ba, to ka koya mini, sai ya ce:
"Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbara, sannan ka karanta abinda ya sawwaka tare da kai na Alkur'ani, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, sannan ka dago har sai ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, sannan ka dago har sai ka natsu a zaune, kuma ka aikata hakan acikin sallarka gaba dayanta".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Lallai ya kasance yana yin kabbara a kowacce sallar farilla da watanta, a Ramadan da waninsa, sai ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa, sannan ya yi kabbara a yayin da yake yin ruku'u, sannan ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan ya ce: Ya Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa kafin ya yi sujjada, sannan ya ce: Allah ne mafi girma a yayin da yake tafiya ƙasa don yin sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa daga zama a raka'a ta biyu, zai aikata haka a kowacce raka'a, har sai ya gama sallar, sannan ya ce a yayin da yake juyawa: na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sallar manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce sallarsa har ya bar duniya.
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai: Akan goshi sai ya yi nuni da hannunsa akan hancinsa, da hannaye, da gwiwoyi, da gefunan diga-digai, kuma kada ka tufke tufafi ko gashi".
Daga Abu Umamah ya ce: Amr ɗan Abasa - Allah Ya yarda da shi - ya zantar da ni cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa kusa da Ubangiji a cikin (kason) dare na karshe, idan kana da ikon ka kasance daga wanda yake ambatan Allah a wannan lokacin to ka kasance".
Daga Jariri dan Abadullahi - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Mun kasance a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya dubi wata a wani dare - yana nufin daren haske -(daran sha hudu ga wata) sai Ya ce: "Lallai cewa ku zaku ga Ubanugijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba zaku wahala ba a ganinsa, idan zaku iya kokarin kada a rinjayeku akan sallarku kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta to ku aikata" sannan ya karanta: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta}".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta
{قل يأيها الكافرون} da {قل هو الله أحد}
a raka'o'i biyu (kafin sallar) Asuba.