- Daga hikimomin ɗaga hannaye a cikin sallah cewa hakan ado ne ga sallah da kuma girmama Allah - tsarki ya tabbatar maSa -.
- Ɗaga hannaye ya tabbata daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - aguri na huɗu a cikin riwayar Abu Humaid al-Sa'idi a wajen Abu Dawud da waninsa, shi ne lokacin tasowa daga tahiyar farko a sallah mai raka'a uku da mai raka'a huɗu.
- Ya tabbata daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi yana ɗaga hannayensa daura da kunnuwansa ba tare da shafa ba, kamar yadda yake a cikin riwayar Malik ɗan Huwairis a cikin Bukhari da Muslim: "Cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi kabbara yana ɗaga hannayensa har sai ya zo dasu daura da kunnuwansa".
- Haɗawa tsakanin Tasmi'i da Tahmidi wannan ya keɓanci liman da mai sallah shi kaɗai ne kawai, amma mamu sai ya ce: Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa.
- Faɗin: "Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa" bayan ruku'u ne kamar yadda ya inganta daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa akwai sigogi huɗu, wannan ɗaya ce daga cikinsu, abin da yafi nutum ya bibiyi wadannan sigogin ya zo da wannan wani lokaci, wani lokacin kuma da wannan.