- Waɗannan rukunan na sallah, ba sa faɗuwa ba da rafkanuwa ba ba kuma da jahilci ba, saboda dalilin umartar mai sallar da sakewa, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai isu da koyar dashi ba (saida ya sashi ya sake).
- Natsuwa rukuni ce daga cikin rukunan sallah.
- Nawawi ya ce: A cikinsa cewa wanda ya ɓata wasu wajiban sallah to sallarsa ba ta inganta ba.
- Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa akwai sauƙaƙawa ga mai neman sani da kuma jahili da sassauta masa, da bayyanar da masa'alar gare shi da rairaye manufofi, da taƙaitawa a matakinsa akan manyan mihimmai banda wadanda suke cikawa waɗanda halinsa ba zai iya ɗaukar iya kiyayesu da kuma tsayuwa da su ba.
- Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa cewa mai bada fatawa idan an tambaye shi game da wani abu, kuma a nan akwai wani abu daban da mai tambayar yake buƙatuwa zuwa gare shi kuma bai tambaye shi ba to an so ga matawar ya faɗa masa shi, kuma wannan ya zama daga nasiha ne ba daga zancen da bai shafe shi ba ne.
- Falalar iƙirari da kasawa saboda faɗinsa; "Ba zan iya yin wacce ta fi ta ba to ka koya mini".
- Ibnu Hajar ya ce: Kuma a cikinsa akwai horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ƙi, da kuma neman mai neman sani daga malami cewa ya koya masa.
- An so yin sallama a lokacin haɗuwa, da kuma wajabcin amsa ta, kuma an so maimaitata idan haɗuwa ta maimaitu koda ba'ajima ba, kuma cewa wajibi ne ya amsa masa a kowane lokaci.