Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ji lad...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya nuna wa wanda ya ji mai kiran sallah da ya maimaita a bayansa, sai ya faɗi irin abinda ya f...
Daga sa'ad Dan Abu Wakkas - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: "Wanda ya ce lok...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah "Ina shaidawa cewa babu abin...
Daga Jbir ɗan Abbdullahi - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Duk wanda ya ce a y...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah bayan ya gama: (Ya Allah Ma’a...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba'a dawo da addu'a tsakani...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana falalar addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama, kuma cewa ba'a dawo da ita kuma ta ca...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum makaho ya zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ya Ma’aikin...
Wani mutum makaho ya zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ya Ma’aikin Allah ! Ba ni da wanda zai taimaka min ya riƙe ha...

Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi masa salati goma da shi, sannan ku roƙi Allah Wasila gareni, domin cewa ita wani matsayi ne a aljanna, ba ya kamata sai ga wani bawa daga bayin Allah, ina ƙaunar in zama ni ne shi, duk wanda ya roƙi Allah Wasila gareni, to, cetona zai tabbata gare shi".

Daga sa'ad Dan Abu Wakkas - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: "Wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, baShi da abokin tarayya, kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, na yadda da Allah Shi ne Ubangiji kuma (Annabi) Muhammad Manzo ne, kuma Musulunci shi ne Addini. Za’a gafarta masa zunubinsa".

Daga Jbir ɗan Abbdullahi - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Duk wanda ya ce a yayin da ya ji kiran sallah: (Ya Allah, Ma’abocin wannan cikakken kira da sallah da za'a tayar, Ka bai wa [Annabi] Muhammad al-Wasila da al-Fadila, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo wanda Ka yi masa alƙawarin sa), ceto na zai halatta a gare shi ranar alƙiyama".

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum makaho ya zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ya Ma’aikin Allah! Ba ni da mai jagora da zai ja ni zuwa Masallaci, sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ya yi masa rangwane da ya yi Sallah a gidansa, sai ya yi masa rangwame, a lokacin da ya juya ya tafi, sai ya kira shi ya ce: shin kana jin kiran Sallah idan aka kira, ya ce: Eh, sai ya ce: Ka amsa.

Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Shin kuna ganin cewa da ace akwai wata korama a kofar dayanku yana wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, shin kuna zatan wani abu na dattinsa zai rage ?" Suka ce: Ba abin da zai rage dattinsa, ya ce: "To hakan tamkar salloli biyar ne, Allah Yana shafe kurakurai da su".

Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafifici a wurin Allah? ya ce: "Sallah akan lokacinta", Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: "Sannan biyayya ga mahaifa" Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: Yaki a tafarkin Allah" ya zantar dani su, da na nemi ya kara min da ya karamin.

Daga Usman -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto shi, sai ya kyautata alwalarta da khushu'inta da ruku'inta, sai ta zama kaffara ga abinda ke gabaninta na zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi ba, hakan a zamani ne gaba dayansa".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce "Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai".

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce: Wasiyyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai gamewa ta kasance lokacin da rasuwarsa ta zo masa: «Ku kula da sallah da abinda hannayenku suka mallaka, ku kula da sallah da abinda hannayenku suka mallaka», har Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara gargarar mutuwa, amma harshensa bai iya faɗinta ba.

Daga Amr Dan Shu'aib daga babansa daga kakansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Allah - maɗaukakin sarki Ya ce: Na raba sallah tsakanina da tsakanin bawaNa gida biyu, bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan bawa ya ce: {Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: bawaNa ya godemin, idan ya ce: {Mai kyauta a duniya mai jin ƙan muminai a lahira}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: BawaNa ya yabeni, idan ya ce: {Mamallakin ranar sakayya}, Zai ce: BawaNa ya girmamaNi, - wani lokaci kuma ya ce: bawaNa ya fawwala (al'amuransa) gareNi -, idan ya ce: {Kai kaɗai muke bautawa, kuma gareka kaɗai muke neman taimako}, sai Ya ce: Wannan tsakanina da tsakanin bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan ya ce: {ka shiryar da mu hanya madaidaiciya, hanyar waɗanda Ka yi ni'ima a garesu ba waɗanda Ka yi fushi a kansu ba, ba kuma ɓatattu ba}, zai ce: Wannan ga bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa".