- Girman sha'anin Fatiha haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - ya ambaceta (Sallah).
- Bayanin kulawar Allah - Maɗaukakin sarki - ga bawanSa, yayin da ya gode maSa sabo da godewarSa da yabonSa da girmamaShi, kuma Ya yi masa alƙawari zai ba shi abin da ya roƙa.
- Wannan surar mai girma ta ƙunshi godiya ga Allah, da ambaton makoma, da roƙon Allah, da tsarkake ibada gareShi, da roƙon shiriya zuwa hanya madaidaiciya, da gargaɗi a kan hanyoyin ƙarya ( bata ) .
- Jin wannan hadisin (ji irin na halarto da ma'anarsa) ga mai sallah - idan ya karanta fatiha - zai ƙara masa khushu'insa a sallarsa.