- Halaccin wannan addu'ar bayan gama maimaita (kiran sallah) a bayan ladan, wanda bai ji kiran sallah ba; to shi ba zai faɗeta ba.
- Matsayin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda aka ba shi Wasila da Fadila da matsayi abin yabo da babban veto a kan rabewa tsakanin halittu.
- Tabbatar da ceto ga Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; saboda faɗinsa: "Cetona ya halatta gare shi ranar alƙiyama".
- Cetonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kasancewa ne ga ma'abota manyan zunubai daga al'ummarsa a cikin rashin shiga wuta ko kuma a fitar da wanda ya shigeta, ko kuma a shiga aljanna ba tare da hisabi ba, ko ɗaukaka darajojin wanda ya shigeta.
- AlƊaibi ya ce: Daga farkonsa zuwa faɗinsa: "(Annabi) Muhammad Manzon Allah ne" ita ce cikakkiyar kira, Hai'ala kuma ita ce sallar da za'a tayar a cikin faɗinsa suna tsaida sallah, za'a iya ɗaukar cewa ya zama abin nufi da sallar addu'a da kuma za'a tayar madawwamiya daga ya tsaya akan abu idan ya dawwama a kansa, akan haka ne to faɗinsa:
- "Da sallah dawwamammiya" bayani ne ga kira cikakke, kuma zai iya ɗaukar cewa ya zama abin nufi da sallar wacce a za’a yi ake kira zuwa gareta a wannan lokacin ita ce mafi bayyana.
- AlMuhallab ya ce: A cikin hadisin akwai kwaɗaitarwa akan yin addu'a a lokutan salloli; domin loakaci ne na fatar amsar Addu’a .