- Girman sha'anin sallah da haƙƙin abinda hannu ya mallaka; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wasicci da su a cikin ƙarshen abinda ya yi wasicci (da shi).
- Sallah tana daga mafi girman haƙƙin Allah akan bayinSa, da kuma bada haƙƙin halitta musamman ma raunana da waɗanda suke ƙarƙashin hannu waɗanda ba iyalai ba yana daga mafi girman haƙƙoƙin halitta.