- Kwaɗaitarwa a kan amsawa mai kiran sallah.
- Falalar salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan amsawa mai kiran sallah
- Kwaɗaitarwa a kan roƙa wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Wasila bayan salati a gareshi .
- Bayanin ma'anar Wasila, da ɗaukakar darajarta ta inda ba ta tabbata sai ga wani bawa ɗaya.
- Bayanin falalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da aka keɓanceshi da wancan babban matsayin.
- Wanda ya roƙi Allah Wasila ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - to, cetonsa zai ya halatta gare Shi.
- Bayanin ƙanƙar da kansa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da ya nemi addu'a daga al'ummarsa na wannan matsayin, tare da cewa zai kasance gare shi.
- Yalwar falalar Allah da rahamarSa, aikin lada ɗaya (za a yi sakamako) da goma tamkarta.