- Sallah mai kankare zunubai ita ce wacce bawa ya kyautata alwalarta, kuma ya yi ta yana mai khushu'i ya nufi yardar Allah - Madaukakin sarki - da ita.
- Falalar dawwama akan ibadu, kuma cewa su sababine na gafarta kananan zunubai.
- Falalar kyautata alwala, da kyautata sallah da khushu'i a cikinta.
- Muhimmancin nisantar manyan zunubai dan gafarta kananan zunubai.
- Manyan zunubai ba'a kankaresu sai da tuba.