Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta
Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta".
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa alƙawari tsakanin musulmai da wasunsu daga kafirai da munafikai (shi ne) sallah, wanda ya barta to haƙiƙa ya kafirta.
Hadeeth benefits
Girman al'amarin sallah, kuma cewa ita ce mai banbantawa tsakanin mumini da kafiri.
Tabbatar da hukunce-hukuncen musulunci da zahiri daga halin mutum ba baɗininsa ba.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others