- An so karanta waɗannan surori biyun bayan fatiha a sunnar (Raka’atal fajr) Asuba.
- Waɗannan surori biyun ana ce musu Suratul Ikhlas; domin a cikin Suratul kafirun akwai kuɓuta daga dukkan abinda mushrikai suke bautawa koma bayan Allah, kuma su ba masu bautar Allah ba ne domin shirkarsu tana ɓata ayyukansu, kuma Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne Mai wanda ya cancanci ibada, kuma cewa a cikin Suratul al-Ikhlas akwai kaɗaita Allah (da bauta) da kuma tsarkake (ibada) gare shi da bayanin siffofinSa.