- Boye addu'ar buɗe sallah koda sallar ta kasance ta karatun bayyana ne.
- Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan sanin halayen Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a motsinsa da shirunsa.
- Wasu sigogin daban sun zo na addu'ar buɗe sallah, abinda ya fi shi ne mutum ya bibiyi addu'o'in buɗe sallah da suka zo, kuma tabbatattu daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya zo da wannan wani lokaci, wani lokacin kuma ya zo da wannan.