- Wanin karatun Fatiha ba ya isarwa daga gareta tare da iko a kanta.
- Bacin raka'ar da ba'a karanta Fatiha a cikinta ba, daga mai ganganci da jahili da mai mantuwa; Domin cewa ita rukuni ce, rukunai ba sa saraya ta kowanne hali.
- Karatun Fatiha yana saraya daga mamu idan ya riski liman yana ruku'u.