- Wajabcin yin sujjada a cikin sallah akan gabbai bakwai.
- Karhancin tattaro tufafi da gashi a cikin sallah.
- Yana wajaba akan mai sallah ya natsu a cikin sallarsa, hakan ya sanya gabban sujjada guda bakwai akan kasa, ya tabbata akansu har ya zo da zikirin da aka shara'anta.
- Hani daga kame gashi (wannan) ya kebanci maza banda mata; domin cewa mace a cikin sallah abar umarta ce da sutaurtawa.