- Kwaɗaitar da musulmi akan zikiri a karshen dare.
- Fifikon lokuta a tsakaninsu ga zikiri da addu'a da sallah.
- Mirik ya ce: A cikin banbanci tsakaknin faɗinsa: "Mafi kusancin lokacin da Ubangiji ya fi kusa da bawa", da tsakanin faɗinsa: " Mafi kusancin lokacin da bawa yake kusa da Ubangijinsa alhali shi yana mai sujjada': Abin nufi a nan bayanin lokacin kasancewar Ubangiji Shi ne mafi kusa ga bawa shi ne tsakiyar dare, abin nufi a can bayanin kusancin halayen bawa ga Ubangiji alhali shi yana halin sujjada.