- Bayanin abin da ake so masallaci ya faɗe shi idan ya ɗago kansa daga ruku'u.
- Halaccin daidaituwa da nutsuwa bayan ɗagowa daga ruku'u; domin cewa ba zai yiwu ba ya faɗi wannan zikirin sai dai idan ya daidaita kuma ya nutsu.
- Wannan zikirin abin shara'antawa ne a dukkanin salloli, duk ɗaya ne ta kasance farilla ce ko nafila.