- Falalar kulawa akan sallar asuba da la'asar; domin asuba tana kasancewa ne a lokacin daɗin bacci, la'asar kuma tana kasancewa ne lokacin shagaltuwar mutum da aikinsa, wanda ya kiyayesu ya kasance mafi cancanta ya kiyaye ragowar salloli.
- An ambaci sallar asuba da la'asar da sanyaya biyu; domin sallar asuba a cikinta akwai sanyin dare, sallar la'asar kuma a cikinta akwai sanyin rana, koda sun kasance a lokaci na zafin rana, saidai wannan lokacin ya fi saukin (zafi) kafin wannan lokacin, ko kuma ambatansu ya zama ta babin rinjayarwa kamar yadda ake cewa: Watanni biyu ga rana da wata.