- Kwaɗaitarwa a kan kiyaye sallar la’asar a farkon lokacinta, da kuma gaggawar yinta.
- Narkon azaba mai tsanani ga wanda ya bar sallar La’asar har loakcita ya fita, kuma barinta har fitar Lokacita ya fi tsanani a kan wata da ba ita ba, domin ita ce Sallah mafificiya wacce aka keɓance ta da umarni a faɗin Allah maɗaukaki: ((Ku kiyaye Salloli kuma ku kiyaye sallah mafificiya)). Bakara, 238.