- Bigiren wannan Tahiyar shi ne zama bayan sujjada ta karshe a kowacce sallah, da kuma bayan raka'a ta biyu a sallah mai raka'a uku da mai raka'a hudu.
- Wajabcin gaishe-gaishe a Tahiya, yana halatta ya yi tahiya da kowanne lafazi daga lafazan tahiya daga abinda ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Halaccin addu'a da abinda mutum ya so muddin dai ba sabo ba ne.
- An so farawa da kai a cikin addu'a.