Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni
Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni.
Bayani
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana yin Addu’a tsakanin sujjada biyu a Sallarsa, da waɗannan addu’o’in biyar, wacce Musulmi yake da matuƙar buƙatar su, kuma sun ƙunshi alheran duniya da lahira, kamar neman gafara, da ɓoye zunubi, da kuma yafe su, da malalo rahama da waraka daga shubuhohi da abubuwan sha’awe-sha’awe da rashin lafiya da cututtuka , da kuma roƙon Allah samun shiriya a kan gaskiya da kuma tabbata a kanta, da arziki na imani da ilimi da aiki na ƙwarai da kuma dukiya ta halal mai daɗi.
Hadeeth benefits
Shar’antuwar wannan Addu’ar a zaman dake tsakanin sujjada biyu.
Falalar wannan Addu’ar saboda abin da ta ƙunsa na alheran duniya da lahira.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others